Matthew 7

Ɗora wa Waɗansu Laifi

1“Kada ku shariʼanta wani, in ba haka ba, ku ma, za a shariʼanta ku. 2Gama da irin shariʼar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shariʼanta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.

3“Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗanʼuwanka, alhali kuwa da gungume a naka ido? 4Yaya za ka ce wa ɗanʼuwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido? 5Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a saʼan nan za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗanʼuwanka.

6“Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu luʼuluʼanku. In kuka yi haka za su tattake su, saʼan nan su juyo su jijji muku ciwo.

Roƙa, Nema, Ƙwanƙwasa

7“Roƙa za a ba ku; nema za ku samu; ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 8Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.

9“Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yǎ ba shi dutse? 10Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yǎ ba shi maciji? 11In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ʼyaʼyanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba! 12Saboda haka, cikin kome ku yi wa waɗansu abin da kuke so su yi muku, gama wannan shi ne duk abin Doka da Annabawa sun kunsa.

Matsattsiya da Faɗaɗɗiyar Ƙofa

13“Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, kuma masu shiga ta cikinta suna da yawa. 14Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.

Itace da ʼYaʼyansa

15“Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne. 16Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? 17Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ʼyaʼya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ʼyaʼya masu kyau. 18Itace mai kyau ba ya ba da munanan ʼyaʼya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ʼyaʼya masu kyau. 19Duk itacen da ba ya ba da ʼyaʼya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta. 20Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”

21“Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji’, ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama. 22Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’ 23Saʼan nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’

Magini Mai Hikima da Marar Hikima

24“Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, domin yana da harsashinsa a kan dutse. 26Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”

28Saʼad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa, 29domin ya koyar kamar wani wanda yake da iko, ba kamar malamansu na dokoki ba.

Copyright information for HauSRK